(ABNA24.com) Kwamandan dakarun dake rike da ikon gabashin kasar Libiya, Marshal Khalifa Haftar, ya sanar a cikin daren jiya Laraba da dakatar da wani farmakin soji a fadin kasar alfarmar wannan wata na Ramadana, kamar yadda kakakinsa ya sanar.
Da yake karanto sanarwar tun daga birnin Benghazi, Ya ce bisa bukatar kasashe aminnai, kwamanda Janar Khalifa Haftar, ya amince tsagaita wuta.
Amma a cewarsa zamu maida martani kan duk wata tsokana idan waccen bangaren ya sabawa shirin tsagaita wutar.
Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan kiran da MDD, da kungiyar tarayyar turai da wasu kasashen duniya sukayi na a tsagaita wuta a kasar ta Libiya alfarmar wannan wata na Ramadana.
Har zuwa lokacin fasara wannan labarin, babu wani maratani daga gwamnatin hadin kan kasa ta Tripoli dake samun goyan bayan MDD.
/129
2 Mayu 2020 - 03:52
Lambar labari: 1032231
Kwamandan dakarun dake rike da ikon gabashin kasar Libiya, Marshal Khalifa Haftar, ya sanar a cikin daren jiya Laraba da dakatar da wani farmakin soji a fadin kasar alfarmar wannan wata na Ramadana, kamar yadda kakakinsa ya sanar.